Spread the love

Sarkin Kaurar Namoda dake cikin jihar Zamfara Alhaji Ahmed Muhammad Asha wanda aka fi sani da Sarkin Kiyawan Kaurar namoda ya rasu da safiyar Lahadi yana da shekarru 71 ya bar duniya.

Kanen margayin Abdulkarim Ahmad Asha Dan jekan Kaurar Namoda ya yi fama da ciwon hawan jini da suga a tsawon lokaci kafin rai ya yi halinsa.

“Akalla ya kwashe sama sda shekarru hudu yana fama da ciwon yana fada jikin ya tashi aka tafi da shi asibitin kwararru ta Yariman Bakura a can ne ya rasu bayan kwana uku da kwantar da shi.” a cewarsa.

Kafin ana da shi Sarkin Kaura a shekarar 2004 ya yi zama daraktan kudi da kuma ma’aji a kanan hukumomi daban-daban a jihar Zamfara.

Ya rasu ya bar matan aure uku da ‘ya’ya 11, cikin akwai soja Sanusi Muhammad Asha wanda a halin yanzu yake Maiduguri jihar Borno.

An yi masa sutura kamar yadda addini ya tanadar an rufe shi a Kaurar Namoda.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *