Spread the love

Wasu daga cikin mutane dake dauke da rashin lafiyar Fiva da wasu kananan cirutoci ba su samu kulawar likitoci, sun fita batunsu, kamar yadda jaridar daily trust ta fahimta.

Aminu Muhammad dake zaune a unguwar Gandun Albasa ya sanar da cewa ya kai mahaifinsa ba shi da lafiya a asibitin koyarwa ta Aminu Kano amma aka ki karbarsa domin a duba lafiyarsa.

Ya ce da gaggawa suka tafi da mahaifinsu asibitin don yana cikin halin neman agajin gaggawa, amma da suka tafi asibitin aka ce babu gadon da za a kwantar da shi, da suka tafi bangaren bayar da agajin gaggawa likitan dake wurin ya kore su daga kusa da shi.

“Mun tsaya dan wani lokaci kafin likita ya yi mana wasu tambayoyi kan halin da mahaifinmu yake ciki. Abin da ya bata min rai bai fi yanda likitan ya hana mana mu zo kusa da shi balle ya duba mahaifinmu, ya sanya wata kujera da muke da tazara mita shidda tsakaninmu da shi, na fada mashi babanmu yana fama da Fiba ne, ya ce mu bar asibitin ba su da gadon da za su kwantar da shi, na dauke shi zuwa asibitin Nasarawa ita ma dai hakan labarin bai canja ba. A karshe dai an kwantar da shi asibitin kwararru ta Murtala Muhammad bayan kwana uku ya rasu” a cewarsa.

Da yawan mutane suna kokawa ne kan marasa lafiya a jihar ba su samun kulawar jami’an lafiya abin da da yawan mutane ke ganin shi ne ke yin sanadiyar rasa rayukkansu.

Mafiyawan mutanen da ke rasa ransu suna fama da Fiba da Maleriya da Taifod, suna bukatar kulawar jami’an lafiya a asibitoci daban daban rashin haka ke zama sanadin rasuwar ta su.

Hajiya Hauwa Muhammad Abdullahi mataimakiyar daraktan sadarwa a asibitin koyarwa ta Aminu Kano ta ce su ba su kin karbar marasa lafiya in aka zo da su, bangarorin asibitin gaba daya suna aiki.

Ta kara da cewar sai dai yanzu suna da yawan marasa lafiya da suke kulawa da shi a rana, hukumar asibitin ta kayyade mutanen da za su ga likita a rana haka ma masu bayar da kulawa ta gaggawa ita kadai ce za su bayar.

Ta ce ba su kin karbar marar lafiya sai dai sun kayade nambar marar lafiyan da za su duba a rana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *