Korona: Muna fuskantar karancin dunki sallah a wannan shekara—Tela a Sokoto

Wani matashi da ya share shekaru 21 yana sana’ar dinki a jihar sokoto Malam Abdulkadir Oga a tattaunawarsa da  Mujallar Managarciya ya ce  ba shakka  shi da takwarorinsa masu dinkin Tela cikin  Sokoto a bana wannan shekara suna fuskantar kalubalen karancin dunkin sallah,  idan aka yi la’akari da halin da ake ciki wanda hakan ne suke ganin ya jawo, matsalar annobar Korona ce da ta sanya komi ya tsaya cik ba wata hidima da ake yi ta samun kudi.

Ya cigaba da cewa “Duk da shekarar bara wadda ta gabata ma ta zo muna da ‘yan matsaloli tau, amma ta bana ita ce shekarar da ke da kalubale da yawa, domin kuwa a duk shekara  a daya ga watan Ramadan na riga na rufe karbar dinki, amma a bana yau muna 10 ga watan Azumi har yanzu ban tsayar da ranar da  zan dakatar da karbar dinki ba”. A cewarsa.

Ya kara da cewa ko kwastomominsa da ke kawo masa dinki har yanzu daya bisa ukku kawai ne suka zo, wadan da suka kawo dinkin ma za ka ga mai yin kala goma ya dawo biyar, mai yin biyar ya dawo yin biyu. Kuma wannan yana da nasaba ne da rashin kudin da ke addabar al’umma.

Ya ce yanzu haka yana da yara 10 dake dinki karkashinsa, kuma duk shekara abokan sana’arsa na neman ya ara musu yaran da za su kama musu aiki, amma a bana har yanzu ba mutun daya da ya nemi ya ara masa ko yaro daya.

Ya bayyana cewa yanzu dai sun zurawa sarautar Allah ido, tare da cigaba da dinkin da ke hannun su kafin wasu su samu, da fatan abubuwa za su warware kowa ya fito ya yi ta hada-hadarsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *