Spread the love

Hukumar ‘yan sanda ta jihar Katsina, karkashin kwamishinan ‘yan sanda Sanusi Buba, sun kama tsoho dan shekara 70 da haihuwa Malam Lawal Abdullahi Izala tare da wasu matasa guda biyu da zargin hada baki, suka zagi Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da Gwamna jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari.

Bidiyon zagin wanda yake yawo a kafar sadarwa ta zamani shi ne dalilin cafke tsohon da matasan biyu.

Bayanin kama wadannan mutane guda ukku, ya zo ne a wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ‘yan Sanda ta jihar Katsina S P Gambo Isah ya rabawa manema labarai a Katsina.

SP Gambo Isa ya kara da cewa ” an ja hankalin rundunar, kan wani bidiyo da ke yawo a kafar sadarwa ta zamani wato (Social Media) inda Lawal Abdullahi, wanda aka fi sani da Alhaji Lawal Izala, dan shekara saba’in da haihuwa dake Unguwar Gafai a cikin birnin Katsina, ke zabga ashar ko zagi ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da kuma Gwamna Aminu Bello Masari”.

Gambo Isa ya cigaba da cewa “Kwamishinan Yan Sanda na jihar Katsina, Sanusi Buba ya ba da umurnin a yi bincike, wanda ya haifar da damke Lawal Izala da wasu matasa guda biyu Bahajaje Abu dan shekara talatin da haihuwa da kuma Hamza Abubakar, dan shekara ashirin da bakwai dukkan su mazauna unguwar Gafai a cikin birnin Katsina.

Rundunar Yan Sanda ta jihar Katsina, za ta cigaba da yin aiki ba dare ba rana, domin ganin ta hukunta bata gari da masu yiwa dokar kasa karan-tsaye. Kuma duk wanda aka Kama yana amfani da kafofin sada zumunci yana cin mutunci mutane da zaginsu zaa hukunta shi kamar yadda doka ta tanada.

Zagin shugabanni ba abu ne mai kyau ba bai kamata talaka ya rika zagin shugabanninsa, amma suma shugabanni yakamata su rika yi masa adalci da rashin cin zarafinsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *