Spread the love

Yakamata mu yi amfani da abin hannunmu don taimakawa talakawa da maras galihu—Honarabul Ubaida Bello

“Hannu daya bai daukar yashi mu ‘yan siyasa bai kamata mu rungumi hanayenmu mu ce sai gwamnati ta bamu kayan rabawa jama’a, sannan za mu ba na kasa gare mu, ya dace mu yi amfani da abin hannunmu don taimakawa talakawa da maras galihu, mu canja tunanin wai sai randa gwamnati ta bayar da kayan azumi, sa’annan mutum zai yi nashi rabon, shi ba zai iya fitar da abin aljihunsa ba, hakan bai kyautu ba, ai ba sai ka yi da yawa ba, ka yi gwargwadon karfinka in na gwamnatin ya zo ka kara in ba zo ba ka yi naka kokarin da mutane za su amfana kamar yadda kake amfana da gwamnati”.

Honarabul Ubaida Muhammad  Bello mai baiwa gwamnan Sokoto shawara kan harkokin kungiyoyin sa-kai da kwato hakkin jama’a ce ta yi wadan nan kalamai a zantawar da Managarciya a satin da yagabata bayan ta kamala rabon kayan azumin watan Ramadan ga mabukata wanda take yi a duk shekara, ta ce bai kamatata ‘yan siyasa su rika tunanin wai sun yi tanadi ne don su ɓoye abin da suke da shi, ba ta taɓa alheri ba ta ji dadi a ranta ba, tana son tainakawa mutumin da ke  cikin wani hali.

Ubaida ta ci gaba da cewa a shekarar nan ta raba wa mutane kayan abinci da suka hada da shinkafa da taliya da suga da man dafuwa sama da mutum 200, bayan kudin da wata abokiyarta ta kawo dubu 176 ta kara domin a sawo kayan ta kashe sama da dubu 780, tana kan rabon tallafin.

Ta shawarci mutane musamman wadan da ba su yarda da cutar Korona ba, “Annoba ba sabon abu ba ne, Korona gaskiya ce, su jingine wannan al’adar ta sai sun ga abu da idonsu suke yarda, su baiwa gwamnatin Sokoto hadin kai don yakar wannan cutar kar ta yi jama’a lahani, gwamna Aminu Waziri Tambuwal yana kokari sosai wurin ganin an samu nasarar yakar cutar a Nijeriya.” a cewarta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *