Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta raba tallafin kuɗi biliyan 43.416 domin zaburar da jihohin da suka cancanta su 24 a cigaban da suka samar a shekarar 2018, a wani shirin bankin duniya kan tafiyar da gwamnati cikin gaskiya da amana.

Ministar kuɗin Nijeriya Malama Zainab Ahmed ta sanar da hakan a wata takarda da daraktan hulɗa da manema labarai Hassan Dodo ya sanyawa hannu a jiya Laraba.

A cewar Minstar jihohin 24 sun haɗa da Abia da Adamawa da Bauchi da Benue da Delta da Edo da Ekiti da Enugu da Gombe da Jigawa da Kaduna.

Sauran su ne Kano da Katsina da Kebbi da Kogi da Kwara da Neja da Ondo da Ogun da Oyo da Osun da Sokoto da Taraba da kuma Yobe.

Ta ce rabon ya biyo bayan cancantar da suka yi ne a wani aiki da ofishin babban mai bincike na tarayya ya gudanar da wasu masu bincike masu zaman kansu.

2 thought on “Sokoto da Kaduna na cikin jihohi 24 da gwamnatin tarayya ta ba su tallafin biliyan 43.4”
 1. Assalamu Alaykum, ya kamata a kullum mu rika mutunta harshen mu, mu daina cin mutuncinsa domin mu burge wasu, kalmar Sokoto Turanci ne, Sakkwato itace kalmar Hausa. Wannan mujallar ina jin dadin zuwan ta kwarai, amma ina son a rika karanta kowanne rubutu tare da yin gyara kafin a sake shi ga mutane. Allah ya kara maku basira da hakuri da juriya da kuma fasaha da tsoron Allah wajen wannan aiki. Ku baiwa dukkanin jam’iyyoyin kasarnan dama, domin ku rika samun tallace tallace a wurin kowa, ka da ku tsaya wajen jam’íyya daya saboda ‘yan siyasa akasarin su ba su da tabbas.

  1. Muna godiya da shawararka, za mu kiyaye sosai
   Amma maganar wata jam’iya daya muke yi wa aiki ba haka ba ne, mun samar da wannan mujalla ne domin fadakarwa da ilmantarwa.
   Kofar mu a bude take ga duk wanda yake son yin mu’amala da mu.
   Mun gode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *