Spread the love

Daga Adamu Aliyu Ngulde a Maiduguri.

Shehun Bama Alhaji Kyari Ibn Ibrahim Elkanemi ya rasu, shi ne sarkin Bama na farko tun sanda aka kirkiri masarautar karkashin mulkin tsohon gwamnan Borno Ali Modu Sharff a watan Maris na shekarar 2010.

Kwamishinan yada labarai da lamurran cikin gida da al’adu Alhaji Baba Kura ya sanar da rasuwar a jiya Litinin cewar Sarkin ya rasu a asibitin koyarwa ta jami’ar Maiduguri bayan gajeriyar rashin lafiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *