Spread the love

Cutar Korona ta kashe mutum 3 a Sakkwato

Mutum uku da ke dauke da cutar Korona sun rasu a yau bayan fama da cutar, ba su samu sun warke ba abin da ya zama a jalinsu.

Gwamnan Sokoto Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya ba da sanarwar rasuwar mutanen ta hannun mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai Muhammad Bello a bayanan da ya rabawa manema labarai a Sokoto.

Ya ce Gwamnan Sakkwato ya ba da sanarwar rasa mutum uku wadan da cutar Korona ta kama.

Mutanen uku a cewar Gwamna suna fama da cirutoci irin   Diabitis da Asma da hawan jin kafin cutar Korona ta kama su a tarihin rayuwarsu.

Gwamnatin jihar Sakkwato ba ta bayar da jerin sunayen wadn da suka rasun ba, har zuwa hada labarin.

A bayanin da  aka  samu cikin mutanen akwai Sahabi Darhela Masau dan sanda ne mai mukamin ASP dake aiki a fadar gwamnatin jihar Sokoto  tsawon lokaci kafin cutar ta same shi a satin da ya gabata.

Majiyar ta ce kafin rasuwarsa yana cikin makusantan Gwamnan jihar Sakkwato Alhaji Aminu Waziri Tambuwal  a cikin jami’an tsaron da ke fadar gwamnatin jiha.

Jami’in tsaron mutum ne mai son jama’a da sakin fuska a tsakanin mutane, a lokacin rayuwarsa mutum ne mai son hulda da manema labarai musamman idan aiki ya kawo su fadar gwamnatin jiha.

Managarciya na cigaba da binciken sauran mutum biyu domin sanar da al’umma su waye su kafin gwamnati ta bayar da bayani a hukumance.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *