Spread the love

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nemi majalisar dattijai ta amince ya karbo wani sabon bashin naira biliyan 850 domin gudanar da wasu manyan aiyukka dake cikin kasafin kudin 2020.

Ya nemi bukatar ne a wata takakarda da shugaban majalisar dattijai Ahmad Lawal ya karanta a zaman majalisar na Talata.

A wasikar Buhari ya nuna yana son ya ciwo bashin ne a babbar kasuwar kayayyaki don ya gudanar da aiki, amma a takardar ba a bayyana aiyukkan da za a sanyawa kudin ba.

Shugaban majalisa ya umarci shugabannin kwamitin kudi da kasafi su hadu domin samo bayanai dalla-dalla kan bukatar bashin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *