Spread the love


Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya rage wa’adin dokar zaman gida da aka sanyawa jihohin Legas da Ogun da Abuja daga ranar 4 ga watan Afrilu kuma za a sassauta dokarShugaba Muhammadu Buhari ya kara mako daya kan dokar kullen da aka saka a jihohin Legas da Ogun da kuma Abuja.


Sai dai daga karfe 9:00 na safiyar Litinin 4 ga watan Mayu, za a sassauta dokar, inda mazauna jihohin za su fara fita daga karfe 6:00 na safe zuwa 8:00 na yamma.


Ya bayyana haka ne a jawabin da ya yi wa ‘yan Najeriya a daren Litinin, ya ce dokar hana tarukka na addini da rayuwa yana nan sai yanda hali ya yi.


Buhari ya ce: “Dokar kulle da ake kai a yanzu za ta ci gaba da aiki a Abuja da Legas da Ogun har sai wadannan sabbin matakan sun fara aiki ranar 2 ga watan Mayun 2020 da karfe 9 na safe.”


“Duba da wannan da kuma shawarwarin kwamitin fadar shugaban kasa na musamman da ke yaki da korona da kungiyar gwamnoni, na nrman umarnin sassauta matakan kulle a Abuja da Legas da Ogun daga ranar Litinin 4 ga watan Mayun 2020.”


“Sai dai wannan sassauci bai shafi Jihar Kano ba.”


“Game da Kano, na bayar da umarnin sanya dokar hana fita tsawon mako biyu da za ta fara aiki nan take. Gwamnatin Tarayya za ta bayar da dukkanin agajin da ake bukata na kayan aiki da kuma tallafi ga mutane domin taimaka wa jihar wurin yaki da annobar korona.”


“Burinmu shi ne mu samar da tsari da zai tabbatar da cewa tattalin arzikinmu ya ci gaba da aiki a yayin da a hannu guda kuma za ku ci gaba da daukar tsauraran matakai kan yaki da annobar cutar korona.

“Wadannan matakai irinsu ne shugabannin kasashe suka dauka a fading duniya.”


“Sai dai bayan wannan sassauci za a sanya tsauraran matakai na tabbatar da yin gwaji da bin sawu, yayin da harkokin kasuwanci da na tattalin arziki kuma za su farfado.”


“Za a ba da damar shiga da fita da kayayyakin bukatu tsakanin jihohi.

“Za mu tabbatar da cewa ana amfani da takunkumin rufe fuska a cikin taron jama’a tare da tabbatar da ana bin dokar bayar da tazara.”


“Amma dokokin hana taron addini da na shakatawa na nan za su ci gaba da aiki. Ana son gwamnatocin jihohi da kungiyoyi su dinga samar da takunkumin rufe fuska ga ‘yan kasa.


Bayan kammala jawabin da yawan ‘yan ƙasa sun nuna rashin gamsuwa ga dokar ta Kano ganin yanda jihar ke fuskantar yawaitar mutuwa ta wasu dalilai da haryanzu hukuma bata bayyanawa duniya mi ke faruwa ba.

Ana kallon lokaci ne da za a bari kanawa su fita domin neman abinci ganin yanda suke shan wahalar matsi da yunwa, kuma gwamnatoci sun gagara taimaka musu da kayan masarufi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *