Gwamnatin jihar Kaduna ta fitar da sanarwar tsawaita dokar hana fita  karin wasu kwanaki 30 domin dakile yaduwar cutar Korona Birus.


Har wayau jihar ta sake sanar da rage ranakun da ta ware ma mutanen  jihar na  fita daga kwanaki biyu Talata da Laraba zuwa kwana daya tal waton kowace Laraba.

 
Ta ce daga yau, ranar Laraba ce kadai aka yarda al’umma su fita, kuma za ta dau tsatsauran mataki ga duk wanda ya saba dokar domin ta kafa kotun tafi da gidanka da zai yanke wa duk wanda aka kama da laifin karya doka hukunci nan take.


Mutanen jihar sun yi kira ga gwamnati ta samar musu da abinci a lungu da sakon jihar domin suna cikin halin matsi da kuncin yunwa.


Da yawan mutane na kallon ba alfanu a rufe mutane ba tare da an samar musu da wadataccen abinci ba, dukkan lahanin da ciyon Korona yake yi a karshe dai rasa rayuwa ce babban tashin hankali, gwamnati ta gujewa tashin hankalin in ta kulle talaka, amma shi daga sanda aka kulle shi aka sanya masa tashin hankali da yake iya sanya a karshe ya rasa ran nasa.


Matukar gwamnati ba ta lura da kiran da talakawa ke yi ba a halin matsi da suke ciki, wannan dokar da aka sanya za ta zama baya ba zane, gwamnati ta biya bukatunta wadanda ake mulka sun kassara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *