Spread the love

Sadiya Usman wadda aka fi sani da Sasi ta ce ba ta da wani buri a rayuwarta bayan samun nasarar kasuwancinta sai ta ga ta kafa Kamfanin sayar da Busasshen kifi a jihar Kebbi.

 Sasi  matashiya ce mai sana’ar sayar da busasshen kifi a garin birnin Kebbi ta samu shahara sosai a harkar  sana’ar ganin yanda ta jingine neman aikin gwamnati ta rungumi wannan sana’ar bayan ta kammala karatunta na digiri.

Ta ce ta shiga wannan sana’a ce domin ta samun abin dogaro da kanta ba sai ta jira aikin gwamnati ba da yake matukar wahalar samu a wannan lokaci abin da ya sa ta rungumi sana’ar da wasu ke kallon ta maza ce, ta fara da sayo kwali biyu na basasshen kifi a garin Yuwuri ta kawo birnin Kebbi ta sayar anan ne sana’ar ta karbe ta ta zama babbar dila.

Sasi ta cigaba da cewa yanzu danyen kifi take sayowa ta gyara shi da kanta ta yi bandarsa ya bushe ta gyara shi har ta kai tana kai shi a Abuja, Kano, Katsina, Kaduna, Bauchi da sauransu.

Ta ce In ana cikin yanayin da akwai kifi kamar lokacin zafi takan sayar da na dubu 300 a yini ko 200 ya danganta, domin a yanayin sanyi ba a samun kifi ana wahalar samunsa sosai ba riba kuma.

“Ga matsalar samun tallafi daga gwamnati domin inganta jarin sana’arka na yi ta  neman  gwamnatin jiha da tarayya da su tallafa min amma abin bai samu ba, akwai lokacin da mataimakin shugaban kasa ya zo Kebbi ni da hannuna na ba shi kifi a lokacin na zaci za a bani tallafin kudin sana’a amma shiru ba labari.” A cewar Sadiya Sasi

Ta cigaba da cewa tana da burin kifinta ya zagaye ko’ina a kasa da wajenta a san da zaman kamfaninta, tana bayar da shawara ga matasa su jingine tunanin don sun yi karatu sai sun yi aikin gwamnati, sana’a tafi aikin gwamnati don ita yanzu ba wani aikin gwamnati da zai sa ta bar sana’arta, don a halin da ake ciki mai mataki irin nata da yake aikin gwamnati ba zai yi harkokin da take yi ba, musamman taimakon ‘yan uwa, da al’umma tana da kusan mutum 100 dake ci kasa gare ta. A hirar da ta yi da mujallar managarciya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *