Shaikh Musa Ayuba Lukuwa sanannen malamin addini ne a Sokoto da labarai suka cika garin Sokoto cewa sai ya yi tafsirin watan azumin Ramadana na bana duk da dokar hana tafsirin da mai girma gwamna ya kafa tare da barazanar duk wanda ya sabawa dokar ba zai sha dadi ba.

A jiya jumu’a dimbin jama’a suna jiran bayanin lokaci da wurin da za gudanar da tafsirin a saman bimbarin jumu’a Shaikh ya bayar da bayanin janye tafsirin kamar yadda aka tsara.

Lukuwa ya ce Sarkin Musulmi ya turo masa  wakillansa, suka ce ya ce a roke shi don Allah ya yi masa alfarmar jinkirta Tafsirin Azumin Ramadana, na bana.

‘Bai kamata na ki yi masa ba tun da ya roka ta hanyar laluma da mutuntuwa, na ce na yi  masa alfarmar.’

Ya cigaba da cewa ‘Na ce kun ji abin da gwamna ya ce a kalamansa! Tau wallahi ni maganarsa ko kadan bata tayar min da hankali ba, don ni ba abin da ake yi min barazana da shi, gidan yari zuwa na nawa kuma, kashewa  ma ba a yimin barazana da ita na isa mutuwa gwamna da Sarki ba wanda nake neman wani abu wurinsu ba a abin da ake yimin barazana da shi.’ In ji Lukuwa.

Ya ce saboda rokon Sarkin musulmi zan janye gudanar da Tafsiri, ba mu gudun jan daga Allah dai ya kare.

“Wallahi ba mu janye Tafsiri don tsoron kowa ba, darajar Sarkin musulmi ta rokon da ya yi muka yi masa alfarmar, shi ko muna rokonsa ya yi mana alfarma duk an ka ga Wata ya yarda, ya yi sanarwa ko da ta sabawa malaman falaki.” A cewar Lukuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *