Spread the love

Sanannen malamin addinin Musulunci a ƙasar Nijeriya  sheikh Abbas Jega, ya yi bincike a duniyar ilmi ya duba manyan litattafai na addinin Musulunci ya gano cewa cutar Coronavirus ba annoba ba ce, masifa ce.

Abbas Jega ya  ce Coronavirus ba annoba ba ce, masifa ne kawai Allah Ya aiko mana ta sanadin wasu domin ya jarrabi duniya sakamakon miyagun zunnubai da ake aikatawa.

Manyan Malaman Musulunci na duniya sun tabbatar da cewa duk cutar da za ta kama mutum ba ta kashe shi ba kasa da kwana uku to wannan cutar ba’a kiranta da cutar annoba, ba annoba ba ce, uwa uba Annabi Muhammad (SAW) ya ce har abada annoba ba zata sake shiga garin Makkah da Madinah ba.


Don haka inda Coronavirus annoba ce to da ba zata shiga garin Makkah da Madinah ba, bayan haka ta kan yi kwanaki sama da uku tana jikin mutum, kuma ana warkewa, ita kuma cutar annoba ba’a warkewa, idan ta kama mutum sai ta kashe.


Malam Abbas Jega yace duk wanda Coronavirus ta kashe shi kar ku ce yayi shahada, ku nema masa gafara da afuwar Allah kawai a  cikin wani Littafi da Anas bin Malik yake magana akan annoba, ya ce cutar da ake kira annoba ita ce cutar da zata kama mutum yanzu yanzu zuwa an jima kadan ta kashe shi, ya ce anyi annoba cikin garin Makkah na tsawon kwana uku, inda an kara kwana uku da cutar sai ta kashe kowa a garin Makkah , mutum 83 suka mutu cikin iyalin Anas bin Malik. 
Ya ce Anas Bin Malik ya ce lokacin da annobar ta yi tsanani a garin Makkah, sai da kowa ya kwashe kayansa da iyalansa aka koma bakin makabarta, ana jiran mutum ya mutu a bunneshi,
Ya ce Coronavirus ba annoba ba ce, masifa ce Allah Ya jarrabi bayinSa da ita, kuma idan kowa ya tuba ya gyara tsakaninsa da Allah sauki zai samu.

Da yawan wasu malamai sun yi raddin wannan fahimta suna ganin cutar a matsayin annoba.

Wasu na ganin hujjojin da malam ya kawo sun isa zama hujja da dogaro kan wannan marhala.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *