Spread the love

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna damuwarsa kan rasuwar Sarkin Malaman Sokoto Shaikh Buhari Siriddawa ya bayyana mutuwar a matsayin rashi ne na kasar gaba daya ba kawai ga mutanen Sokoto ba.

A sakon ta’aziya wanda mataimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai Malam Garba Shehu ya fitar a Abuja a ranar Assabar, ya bayyana gudunmuwar da Sarkin Malaman ya bayar ga samun wanzuwar zaman lafiya a kasar Nijeriya.

Shugaban kasa ya ce “Na samu labarin rasuwar Siriddawa abin ya girgizani matuka, Margayi yana cikin jagororin addini da muke da su a cikin tarihin nan namu da ba za a manta da su ba.”

Shugaban kasa ya ce margayi ya bayar da gudunmuwar samun hadin kai da fahimtar juna a tsakanin mabiya addinai a kasar nan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *