Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar ya ba da sanarwa ganin watan Ramadan a yau Alhamis ya ce sun samu labarin ganin wata daga shugabanni addini da kungiyoyi daban daban a Nijeriya.


Ya roki musulmai su yaiwata addu’a acikin wannan watan  kan kawo karshen wannan annobar ta cutar Korona.


“ina kira ga mutane su bi umarnin da jami’an lafiya da gwamnatoci suka sanya kan kare kamuwar da cutar korona.”Sarkin musulmi bai zayyano garuruwan da aka ga watan ba, amma ya ce kwamitin ganin watan sun tantance sahihancin duk bayanin da aka samu kafin akawo maganar gaban shi.

Sarkin Musulmin ya ba da sanarwar ganin watan a cikin fadarsa cikin tsattsauran matakan hana kamuwa da cutar Korona.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *