Spread the love

Gwamnatin Sokoto za ta haɗa kai da Sarakunan gargajiya a jihar domin hana matafiya shigowa gari

Kwamishinan lafiya kuma shugaban kwamitin  gwamnatin Sokoto kan cutar Korona  Dakta Muhammad Ali Inname ya ce za su hada kai da sarakunan gargajiya domin shawo kan shigowa da matafiya ke yi a jihar bayan an rufe ta, ba za su lamunce wannan lamarin ba. 

“cibiyar horas da masu yi wa kasa hidima NYSC dake Wamakko mun mayar da ita wurin killace wadan da suka shigo jihar nan ta barauniyar hanya za a ajiye su a duba yanayin lafiyarsu kafin a bari su tafi, mun karbi kira yafi 100 kan cutar korona abin da ke nuna mutane sun fadaka da yarda da ciwon nan gaskiya ne a hada kai domin yakarsa.” a cewarsa.

ya fadawa al’umma su kwantar da hankalinsu majiyancin da aka samu da cutar Korona yana murmurewa, kuma suna kan aikin tattara duk wanda mai cutar ya yi mu’amala da su domin yi wa tufkar hanci.

Inname ya nuna sun tsundumma sosai wajen gano in da cutar ta samu wannan mutumin ganin ba in da ya fita, nan da kwana biyu za a samar da cibiya don fara gwajin cutar a Sokoto domin bukatar  yanda za a shawo hana bazuwar cutar.

Kwamishina ya bayyanawa al’ummar Sakkwato  Alhaji Musa Bashar wanda aka fi sani da Rahamaniya a labarin da suka samu ya koma Abuja kamar yadda gwamna ya bukata bai shigo  ba.

Kwamishina ya ce a zuwa yanzu ba su gama haɗa yawan mutanen da suka yi hulda da shi ba amma da zaran sun gama za su yi wa al’umma bayanin yawan da halin da ake ciki.

Ya ce sun fara yiwa asibitocin gwamnati feshin kashe kwayoyin cutar, sun soma magana da asibitoci masu zaman kansu kan yin feshin ita ma wannan hanya ce ta kare yaduwar cutar. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *