Spread the love

Daga Comr Abba Sani Pantami.

Kungiyar gwamnonin Arewa ta dage kan cewa ya zama dole a haramta Almajiranci a yankin kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Gwamnonin sun bayyana hakan ne a ranar Talata yayin da suke tattaunawa kan matakan da yankin za ta dauka don yaki da annobar coronavirus.

Shugaban kungiyar, Gwamna Simon Lalong na jihar Filato ne ya jagoranci taron da gwamnonin 17 suka gudanar ta hanyar amfani da intanet.

Gwamnonin sun kuma tattauna hatsarin da Almajirai ke ciki sakamakon bullar coronavirus inda dukkansu suka amince a haramta almajiranci kuma a mayar da yaran zuwa gidajen iyayensu ko jihohinsu na asali.

Sun dau alwashin cewa ba za su bari a cigaba da almajirancin ba, duba da irin kallubalen da ya ke haifar wa da suka hada da talauci, rashin ilimi, rashin tsaro da rashin tarbiya.

Wannan matakin ya zo daidai lokacin da ake daukar matakan hana kamuwa da cutar ga sauran jama’a.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *