Spread the love


Kungiyar da aka sani da sunan  ‘Islamic Preaching and Public Services-IPPS’ ta ƙasa mai hidikwata a Sokoto  ta  bayar da tallafin kayan abinci ga mabukata mata  zawarawa da marayu da kuma masu lalura dukansu a Jihar Sokoto.


Tallafin wanda shugaban ƙungiyar na ƙasa Malam Jamilu Sani Rarah ya jagoranta ya   Kunshi buhun Shinkafa karami,  Gero da Lita biyu na Man gyada, da suga da kuma Garin wake na yin Kosai, haka aka baiwa kowa cikin mutum 150 da suka amfana.


 kwamishinan ma’aikatar jin dadin Jama’ah ta sokoto Farfesa Aisha Madawaki ta yi kira ga wasu kungiyoyi su yi koyi da kungiyar a haujin tallafawa domin abu mai kyau da zai faranta rai.


 Malamin nan ma Addini Dakta Jabir Sani Maihula ya Jan hankullan Al’umma akan taimakawa mabukata musamman a Irin wannan lokaci na Musibu tare da Kira ga wanyanda ke da abinci Idan sunga ana bayarwa tau su Hankura ka da suje karba domin hakan zai tauye wasu da yawan gaske.


A farko Jamilu Sani Rarah Sokoto Ya Bayyana Adadin waɗan da suka amfana da wannan tallafin Kimanin mutum 150 tare da Yin kira ga sauran kungiyoyi su shigo cikin lamarin don Suma Suna da irin rawar da zasu taka, a taimaki al’umma.


Rarah ya godewa mambobinsu a dukan Arewa ga irin haɗin kan da suke samu wanda shi ne ke ƙara bunkasa ƙungiyar aka santa ko’ina da bayar da tallafi ga al’umma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *