Spread the love

Gwamnan jihar Sokoto   ya ba da sanarwa a wani bayani da aka rabawa  manema labarai a Sokoto, in da yake cewa yana bakincikin sanar da al’ummar jiha an samu bullar cutar Korona a  Sokoto.

Ya cigaba da cewa Mutumin da ya kamu da cutar ya fara  karbar magani  a asibitin koyarwa ta Usman Danfodiyo dake birnin jiha,  bayan an tabbatar yana dauke da cutar an kai shi cibiyar  killacewa da bayar da magani ta Amanawa.

Gwamnan ya nemi mutanen jiha su zama masu biyar doka  ga duk matakin da jami’an lafiya za su dauka don ganin cutar ba ta barbazu ba, ita dai wannan cutar  gaskiya ce.

Tambuwal a kalamansa  ya ce  ‘abin da muke ji ne yanzu kuma ya zo mana akwai bukatar mu tashi tsaye a gwamnati da mutanen jiha mu ga wannan cutar ba ta watsu ba, ina kira ga jama’a su girmama duk matakin da za mu dauka idan lokacin yin hakan ya taso domin samar da kubutar jama’a gaba daya a jiha, akwai yiwuwar daukar matakai nan gaba.’ A cewar shi.

Hankalin Sakkwatawa ya tashi matuka da samun labarin domin bayan fargabar cutar akwai ta hana fita da suke tsoron ka da gwamnatin Tambuwal  ta bi sahun jihohin Kaduna da Kano ganin yanda mutanen ke shan bakar wahala musamman talakawa.

Managarciya ta yi la’akari da yanda hankalin jama’a ya tashi kan halin da ake ciki, suna jin tsoron kar dai rufe jihar ne za a yi ganin yanda gwamnati ba ta da wani mataki na hana yaduwar ciyon sama da rufe mutane a gidajensu, ko da yunwa na damunsu an fi bukatar su tsaya a gida da su kamu da cutar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *