Spread the love

‘Yan sandan jihar Zamfara sun tabbatar da mutuwar mutum 10 wadan da suke fasinja ne a haɗarin motar da ya auku a Kasuwar daji kan hanyar Gusau.

Mai magan da ƴawun hukumar Muhammad Shehu a bayanin da ya fitar ya ce sauran fasinjojin 45 ne suka sami raunuka daban-daban a hadarin da ya faru ranar Assabar da dare.

A shekaran jiya babbar mota na dauke da kayan abinci da mutane ta fito daga kasuwar daji ta yi mummunan hatsari.

Hatsarin ya ci rayuwar mutum 10 nan take mitum 45 suka yi rauni. Shehu ya ce.

Za a yi bincike kan musabbabin lamarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *