Spread the love

Gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya ba da umarni ga jami’an tsaro su tabbatar da sun hana hamshakin dan kasuwa wanda yake dan jihar ne ya shigo cikin garin Sakkwato domin an tabbatar da dansa yana dauke da cutar Korona, don haka shi bai kamata ya shigo ba sai hukumomin lafiya sun gwada shi, don haka na fada mashi ya koma in da ya fito.

Gwamnan ya ba da umarnin ne a yau Litinin a fadar gwamnatin jiha.

A cewar Tambuwal a lokacin da na sami labarin Alhaji Musa Bashar wanda aka fi sani da Rahamiyya cewa ɗansa Abubakar da ya dawo daga Dubai ya kamu da cutar Korona na kira shi na shawarce sa kar ya shigo Sokoto

“na kira shi a waya sau biyu na roƙe shi kar ya shigo jihar nan. Amma ya ce sai ya zo, kan haka na bayar da umarni ga jami’an tsaro su zama a fadake, in ya zo kar su bari ya shigo in ya ƙi su kama shi zan yi duk abin da yakamata don kare mutanen Sokoto.

Gwamna ya shawarci duk wanda yake da alaƙa da shi ya yi masa magana kar ya shigo Sokoto ya yi zamansa Abuja har sai jami’an lafiya sun gwada shi.

Managarciya ta so jin ta bakin Alhaji Musa Bashar wayarsa ba ta shiga za mu kawo bayanin ɓangarensa da zaran mun same shi ta waya ko a fili.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *