Spread the love

Da yawan mutane magidanta a kauyen Danmusa da Dutsinma da Safana kananan hukumomi a jihar Katsina an kashe su in da wasu suka samu rauni sanadiyar hare-haren da aka kawo a safiyar Assabar.

Harin ya sanya da yawan magidanta sun bar garuruwansu.

Akalla an samu labarin mutum 36 ne suka mutu a kauyukkan da yawan mutane suka samu rauni, an lalata kayan miliyoyin nairori a yankin. Da yawan mutane ba a san in da suke ba sun bace ba wani labari kansu.

An kawo harin da misalin karfe uku na daren jumu’a abin ya bazu zuwa sauran kauyukka 10 na kananan hukkumomin guda uku har zuwa 10 na safen Assabar.

Mai magana da yawun ‘yan sanda SP Gambo Isah bai amsa tambayoyin da aka yi masa ba har zuwa hada rahoton.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *