Spread the love

Gwamna Badaru Abubakar, na Jihar Jigawa ya tabbatar da samun mutum daya mai dauke da cutar Covid19 a karamar hukumar Kazaure dake jihar Jigawa.

Tuni Gwamna Badaru ya ba da umarnin hana zirga-zirga a karamar hukumar ta Kazaure, daga daren ranar Latinin har zuwa mako daya.

Gwamna Badaru ya sanar da hakan ne a daren yau Lahadi a birnin Dutse na jihar Jigawa, yayin da yake hira da manema labarai.

Wannan cutar ba karamar barazana ce ga talakawan Nijeriya ba domin tana Kara sanya suna shiga cikin matsi da kuncin rayuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *