Spread the love

Al’umma  da  Gwamnatin Sokoto sun shiga rudu da labarin da suka samu na rasuwar shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya Malam Abba Kyari a jiya Jumu’a ne ya bar duniya.

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na Sokoto a bayanin ta’aziyar  da ya fitar wanda ya sanyawa hannu da kansa ya ce wannan lamarin abin damuwa ne, an rasa kwararre a tafiyar da tsarin shugabanci, Korona da ta kama shi bai samu ya kubuta ba ya rasa ransa kan cutar. 

Gwamna Tambuwal  ya ce mutuwar Abba babban gibi ne ba ga ofis din da yake rike ba kawai, ga kasa baki daya  ya barsu da tunanin halin da ake ciki musamman na wannan annobar.

  Amadadin al’ummar jihar Sokoto suna mika ta’aziyarsu ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari da iyalan margayin da al’ummar jihar Borno gaba daya kan wannan babban rashi da aka yi. Sakon Tambuwal na Ta’ziya. 

Ya roki Allah ya gafarta masa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *