Spread the love

Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko Sarkin Yamman Sokoto ya yiwa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, da Iyalai da daukacin ‘Yan Nijeriya gaisuwar rasuwar Marigayi Shugaban Ma’aikatan fadar Gwamnatin Tarayya Mallam Abba kyari Wanda Allah ya yiwa rasuwa a cikin Daren jiya Jumu’a.

Sanata Wamakko Mai wakiltar kananan hukumomin Sokoto ta Arewa a Majalisar dattawa ta Kasa ya nuna kaduwar sa ainun kan labarin da ya samu na rasuwar Mallam Abba kyari, wanda yake makusanci ne ga Shugaba Buhari.

Kamar yadda ya fada, ” Mutuwa rigar kowa ce, saboda Haka duk rayuwa sai ta dandaneta lokacin da duk Allah ya aiko ta”.

Ya Kara da cewa, ” Ba wani abu da zamu iya yi illa mu maida al’amarin mu ga Allah Ubangiji Mai tsarki”.

Ya ci gaba yana cewa, ” Daidai wannan lokacin da mu muke jimamin mutuwar Abba kyari, Ina Mika sakon gaisuwar Ta’aziyyar rasuwar Mallam Abba kyari Haka Kuma Ina isar da gaisuwar Ta’aziyya ta ga Iyalan sa da dukkan ‘Yan Nijeriya kan wannan gagarumin rashin.

Wannan bayanin na tare da Sa Hannun Bashir Rabe Mani Dan Masanin Mani amadadin Sanatan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *