Spread the love

Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Malam Abba Kyari ya rasu a jiya Jumu’a.

Fadar shugaban kasa ta tabbatar da rasuwarsa ta hannun mai magana da yawun shugaban kasa Malam Garba Shehu in da ya sanarwa mutanen kasa labarin a turakarsa ta facebook.

Ya ce Malam Abba Kyari da ya kamu da cutar Korona ya rasu a yau(jumu’a) jiya kenan.

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya yi ta’aziyar rasuwar margayin a turakarsa ta facebook.

Da yawan ‘yan Nijeriya sun kadu da mutuwar musamman ganin ciwon da ya zama sanadinsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *