Spread the love

Mai girma gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya kori kwamishinansa na ayyuka Injiniya Mu’azu Magaji daga kan muƙaminsa biyo bayan kalaman murnar mutuwar shugaban ma’aikata na fadar shugaban ƙasa marigayi Abba Kyari da ya yi a shafinsa na (Facebook).

A sanarwar da kwamishinan yaɗa labarai Malam Muhammad Garba ya fitar, gwamna Ganduje ya bayyana cewa abin da kwamishinan ya aikata na murna da mutuwar Kyarin ba abu ne mai kyau ba, ya saɓa ƙa’ida, kuma abu ne wanda gwamnatinsa ba za ta zuba ido ta ƙyale mutum mai muƙami a cikinta ya na aikata su saboda wata manufa tasa ta ƙashin kai ba.

Mutane sun yaba da matakin da Gwamna ya dauka domin abin da tsohon kwamishinan ya aikata bai dace ba, ya za ka yi farinciki da abin da zai same ka da Wanda ya mutu da Wanda ke raye dukkansu sai sun mutu to ina abin murna a nan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *