Spread the love

Malam Abba Kyari ya rasu a jiya Jumu’a a jihar Lagos, an kawo gawarsa da safen yau Assabar a difens Hawus dake Abuja domin yi masa sutura.

Shaikh Isa Ali Fantami ne ya jagoranci yi masa sallah domin kai sa makwancinsa, an yi masa sallah a cikin motar da aka sanya gawarsa ba tare da an fito da shi ba, bayan kammala sallar an fita da shi don kai shi makabarta.

An rufe margayin a kwancinsa babu zaman karbar gaisuwar ta’aziya ta margayin kamar yadda fadar shugaban kasa ta fadi.

Malam Garba Shehu mai magana da yawun shugaban kasa a cikin hali na jimame lokacin da yake zantawa da gidan talabijin na kasa waton NTA ya ce ba wani taro na karbar gaisuwa da za a yi, kowa ya yi zamansa in da yake ya yi wa margayin addu’a.

Cutar Korona wadda ta zama sanadin rasa ransa ta hana a yi zaman karbar gaisuwar ta’aziyarsa, an bukaci a yi masa addu’a a gida, ba tare da ka zo wajen makusantansa ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *