Spread the love

Hukumar gidan Yari ta kasa ta yi jifa da jitajitar da ake yadawa wadanda ba gaskiya ba ne cewa Maryam Sanda na cikin mutane 70 da shugaban kasa ya yi wa afuwa a satin da ya gabata.

Hukumar ta tabbatar da babu kamshin gaskiya ga abin da ake yadawa cewa an sake ta.

Sanda an yanke mata hukuncin kisa a ranar 27 ga Junairun wannan shekara wanda babbar Kotun Abuja ta yi kan ta kama ta da laifin kashe mijinta Bilyaminu Bello, ta aikata laifin ne a 19 ga Nuwamban 2017.

Maryam an gurfanar da ita Kotu su tare da mahaifiyarta da dan uwanta, kotu ta sake su domin mai gabatar da kara ya kasa bayyanawa karara in da mutanen suka shiga cikin kisan da Maryam ta yi.

Mai magana da yawun hukumar mataimakin Konturola Augustine Njoku a bayanin da ya fitar ya tabbatar da har yanzu Maryam na cikin komarsu a tsare, ba ta cikin mutum 70 da ake tsare da su a gidan Yarin Kuje da suka ci albarkar afuwar shugaban kasa, ita ba ta cancanta da hakan ba. in ji Njoku.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *