Spread the love

Saboda fara azumin Ramadan Gwamnan Borno ya biya albashi da Fansho na watan Afirilu.


Ma’aikatan gwamnati da masu karbar fansho a jihar Borno sun fara karbar albashinsu na watan Afirilu biyo bayan umarnin da gwamna Babagana Umara Zulum ya bayar a biya,  saboda musulmai su fara shirin watan Ramadana da sauri.
Ana sa ran fara Azumi a sati Mai zuwa, Mai Magana da yawun gwamna Malam Isa Gusau ya ce fitar da lamarin nada manufar daukar mataki kan Korona. 


Gusau ya ce wannan amincewa ta gwamna Zulum matsayarsa ce ta biyan albashi baya cikin nasarorin da gwamnati ta samu don ta biya bashin da ma’aikata ke binta,  yarjejeniya ce tsakanin  mutane da geamnati. 

Gwamna yana biyan albashi a kowane wata daga 26 ga wata a yanzu ya fara biyan ne domin akwai muhimmin lamari a gaban mutane da ya Shafi ibada. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *