Spread the love


Waƙilinmu na jihar Borno Adamu ALiyu Ngulde, ya tattauana da shugaban gidauniyar Borno Reality Empowerment Initiative Kwamared Muhammad Abba Tijjani, ga yadda hirar ta su ta kasance.


Managarciya; Da farko ka gabatar wa mai karatu kanka?

Sunana Kwamared Muhammad Abba Tijjani, an haifeni a tsohuwar unguwar birnin Maiduguri, wadda aka fi sani da Old Maiduguri A ranar 3 ga watan Oktoba na shekarar 1972 na yi karatun firamare a makarantar State Low-cost a shekarar 1978, saannan na shiga makarantar sakandare na Arabic Teachers College a shekarar 1981 na kammala a shekarar 1981 daganan na yi a NCE a kwalejin Sir Kashim Ibrahim, na kamala a
shekarar 2002 daga nan sai na tafi jamiar Maiduguri inda na karanta harkokin gudanarwa Public Admin.

Managarciya: Bayan ka kammala karatunka ka taba aikin gwmanati, mai karatu zai so sanin nauukan aikace-aikacen wannan ƙungiya da ka ke jagoranta?
Eh, na yi aikin koyarwa a shekarar 1997 a makarantar firamare.
Mun kafa wannan gidauniya ne a shekarar 2016 saboda mu taimaka wa masu ƙaramin karfi, kuma hakan ya zo ne bayan tatttaunawa da tarrurukan da muka yi da abokan arziki mun nasarar samun mafitar cewa ya dace mu bayar da tamu gudumawa tare da taimakon junanmu (taken mu shi ne: ta ya za mu yi mu taimaki junanmu). Wanda a karon farko sai muka ɗauki matakin koyar da ilimin na’ura mai ƙwaƙwalwa waton kwamfuta da sana’o’in hannu.


Managarciya: Waɗanne hanyoyi ku ke bi don samun mutanen da ku ke ba su horon koyar da su sanaoin?
Da farko mun fitar da fom da kuma sanar da jama’a cewa duk mai bukatar koyon sana’o’in hannu za su iya saya a ofishinmu dake titin Baga wato daura da Musari. Duk wanda ya sayi fam ɗin muna da sana’o’in da muke koyarwa masu yawan gaske sai mutum ya zaɓi wadda yake da buƙata cikinsu kuwa akwai koyon ilimin kwamfuta, koyon tukin mota, aikin kafinta, gyara naura mai amfnai da hasken rana, kiwon kifi, koyon girki, girke-girke, da kuma yadda za a kawata daki da sauransu.
Saboda ba mu da cibiyar horas da sana’o’in hannu mallakinmu sai mu fita gari domin mu nemi haya mu kai makarantun da muke koyar da matasan. Idan na koma baya da farko muna rubuta takarda zuwa ga ma’aikatar ilimi ta jihar Borno domin a bamu dama mu koyar da matasan. A halin yanzu da nake Magana da kai gidauniyarmu ta koyar da matasa fiye da dubu uku sanaoin hannu, abin alfahari ne a yau sanadiyyar gidauniyarmu akwai wani matashi bayan mun koyar da shi gyara naurar tauraron ɗan adam mai amfani da hasken rana da shi ya yi aure kuma sana’arce ta rike shi.

Managarciya: Bayan kun kammala ba da horon kuna ba da shaidar da mutum zai riƙe a matsayin shaidar koyon aiki(certificate)?
Aikin wannan gidauniyar shi ne bayar da horo kuma ta bai wa waɗanda su ka kammala horon shaida, wanda zai tabbatar da cewa a wurin mu ka koyi sana’ar, mun yi rijista da ma’aikatar yaƙi da talauci ta jihar Borno Kuma kwamishinan ma’aikatar Onarabul Nuhu Clark ya ba mu tabbatacin ma’aikatar za ta dafawa giduaniyarmu, akwai wani lokaci wata ƙungiya mai suna Amtel Charity Foundation ta taɓa tallafawa waɗanda muka koyar mutum fiye da 600 da kayan koyon sana’a domin su tallafawa kansu da kansu.

Managarciya; Gwamnatin jihar Borno tana tallafawa matasa domin ganin an rage talauci hakazalika sanin kowane yanayin da jihar Borno ke ciki akwai buƙatar matasan su bada haimma, Ko kun taɓa ƙoƙarin ganin kun yi haɗin gwiwa da ƙungiyoyi masu zaman kansu domin a yaƙi talaucin nan?
Gaskiya ba mu taɓa yin wani ƙoƙarin neman wata ƙungiya da sunan tallafi ba. Mu dai kawai abin da mu ke yi a kodayaushe shi ne muna gudanar da ayyukanmu da kuma amfani da kafafen sadarwa domin ganin mun yada manufofinmu.
Ba mu da tabbacin ko saƙonmu ya kai in da ya dace, Kuma mun sha rubuta takardu da kuma hotunan ayyukanmu muna aikewa zuwa ma’aikatar gwamnati amma sai dai har yanzun babu wanda ya tuntuɓemu ya bamu ko da kudi ne a hannu baya ga giduaniyar Amtel ‘’Charity Foundation’.

Managarciya: Tsawon wane lokaci mutum zai yi kafin ya koyi wannan horon, kuma nawa ake biya kafin smaun damar koyon sana’o’i a gidauniyar Reality?
Makwanni biyar muke yi domin mu koyar da su, makon farko rijista muke yi, sauran makwannin huɗun su ne mu ke bayar da horo a ciki. Wanda suka hada da karatu tare da gwajin ƙwazon su, kuma kamar yadda na faɗa tun da farko a waje muke neman kayayyakin aiki da kuma kwararrun malaman da za su koyar,
kowane dalibi zai biya naira dubu 3,500. Ka ga anan idan ka lura muna yi ne kawai don mu taimaki al’ummar jihar mu wadda iftilain mayaƙan Boko Haram ya rutsa da su. Har ila yau, mun taɓa shaidawa shugaban kwamitn tsaro na majalisar dokokin jihar Borno Alhaji Ali Kotoko domin neman nasa tallafin na ganin an tallafawa matasa, da kuma wasu masu hannu da shuni da su dafa mana domin mu koyar da su sana’o’in hannu, saboda mu taimaki alummar jihar Borno.

Managarciya; A ƙoƙarin da ku ke yi domin cigaban jihar Borno, kun taɓa neman tallafin gwamna ko wnai na kusa dashi domin a dafawa gidauniyarku?
A’a, gaskiya ba mu gwada ba, amma mun taɓa kokarin yin hakan ta hannun kwamishinan ma’aikatar yaki da talauci na jihar Borno Nuhu Clark ya yi mana alƙawarin zai haɗa mu da ƙungiyoyin aikin ba da agaji na ƙasashen waje da suke zuwa Maiduguri, sai dai har yanzun bamu cire tsammani ba.

Managarciya; Kafin mu fara wannan tattauanawar naji kana maganar ba da bashin filaye, shin yaya tsarin yake ne.
Eh, haka ne muna bai wa jama’a bashin filaye, kuma babu wani nuna bambanci na kai ma’aikaci ne ko ɗan kasuwa; ƙarami da babba, muna yinsa ne ga mai rabo. Matukar ka cika sharuddanmu da kuma ƙa’idoji insha Allahu za mu samar maka da fili kuma cikin watanni 12 wato shekara guda kenan mutum zai biya, iya ƙarfinka za a samarmaka fili guda ko rabin fili duk muna da shi.

Managarciya; Idan mutum bai samu zarafin biya ba har wa’adinsa ya yi ina mafita?

To, idan lokacin ya yi mutum bai iya biya ba, za mu rubuta mashi cewa lokacinka ya wuce don haka ba zamu amince da wannan tsarin ba, sai mu bashi fili iya kudinda ya biya.

Managarciya; Daga ƙarshe ina shawara ga matasan jihar Borno?
Kirana ga matasa shi ne su tashi tsaye domin dogaro da kai ba tare da sun jira wani ko gwamnati ba, sabida a yanzu lokacin dogaro da wani ya wuce, kuma matasa su sani cewa raina sana’a hanya ne na sanyawa mutum tunanin hanyar samun kudi wadda bata dace ba kuma watarana zai iya yin da na sani. Allah ya kiya ye.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *