Spread the love

Mahara dauke da makamai sun yi garkuwa da manyan mata masu reno a gida su uku a Karaukarau cikin karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna, jaridar Nation ta bayyana haka.

Wata majiya daga kauyen ya fadawa manema labarai maharan dauke da muggan makamai sun shigo kauyen a ranar Talata da rana a lokacin da ake bukin aure suka kama mace 13.

Ya ce kar ka mance dokar hana fita da aka sanya a Kaduna kan cutar Korona ta kawowa maharan tsaiko ga samun abinci, kan haka suke zuwa taron bukin aure da makamantansu.

Ya ce a ranar Talata da suka shigo wurin bukin sun dauki mace 13, amma mutanen gari ba su tsorata ba sun hadu suka yunkura Allah ya taimake su suka kubutar da mace 10, in da barayin sun tafi da mace uku masu reno a gidajensu.

Har zuwa hada labarin mace uku na can tare da su.

Mai magana da yawun ‘yan sanda ASP Muhammad Jalige ya ce ba zai ce komai kan lamarin ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *