Spread the love

Daga Muhammad Nasir

Jihohin da ba su da annobar Korona tau su shirya mata, cibiyar kula da ciruta ta Nijeriya ta yi wannan gargadin.

Kwamitin kula da annobar wanda shugaban kasa ya kafa kan ciwon na COVID-19 shi ma a jiya ya ce al’umma suna watsa cutar kusan ko’ina a yanzu, in da abin yafi kamari mutanen da ke tafiye-tafiye a jihohin da bana su ba.

Kodineta na kasa a PTF Sani Aliyu ya ce sun fahimci al’umma na yada cutar akan iyakokin jihohin kasa da ake tafiye-tafiye. Akwai bukatar hana fita wajen jiha don a hana mutane yada wannan cutar, musamman dubi wannan labari da aka yi sumogal din mutane a babbar mota za a fita da su wajen Lagos.

Annobar ta shiga jihohi 19 har da Abuja, jihohi 17 daga cikinsu ba su da cutar kafin dan kasar Italiya ya shigo da ita daga Milan a 27 ga watan Fabarairu.

Jihohi 14 da babu cutar a wurinsu su ne Bayelsa, Cross River, Imo, Ebonyi, Abia, Jigawa, da Zamfara.

Sauran su ne Kebbi, Sokoto, Adamawa, Taraba, Yobe, Borno, Gombe, Kogi, Nasarawa da Filato.

Babban Darakta na cibiyar Chikwe Ihekweazu ya ce a yanzu COVID-19 tana cikin mafiyawan jihohi za ta iya mamaye jihohin Nijeriya, ba wanda zai ce haka ba zai faru ba, za ta mamaye kasar nan ba tantama kan haka, a fuskanci abin da yake shi ne gaskiya wannan annoba ce ciwon nan.

Ya ce abin da ke gabansu Nijeriya ta shirya sosai ta iya karewa da katangancewa da jurewa, ta san wadan da ke da cutar ta hana yada ta.

Managarciya ta fahimci wannan bayani ba zai yi wa jihohin dadi ba amma tun da gaskiya ne ba yanda suka iya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *