Spread the love

Jagoran jam’iyyar APC na kasa, Sanata Bola Tinubu, ya bukaci gwamnatin tarayya ta yi amfani da lambar tantance asusun banki (BVN) wajen aika wa ‘yan Nijeriya kudin tallafin rage radadin matsin da annobar covid-19 ta haifar. 


Tinubu, tsohon gwamnan jihar Legas, ya bayar da wannan shawara ne a cikin wani jawabi da ya fitar ranar Laraba a Legas. Ya ce za a iya biyan kudi kai tsaye zuwa asusun wadanda za su ci moriyar tallafin ta hanyar amfani da BVN dinsu. 


Jagoran na APC ya kara da cewa za a fi samun tsaro ta hanyar tura kudi zuwa asusu tare da bayyana cewa hakan zai kawo karshen rigingimun da ake samu yayin rabon kudin hannu da hannu. 


Tinubu ya ce yin hakan zai kara jawo dumbin jama’a, musamman talakawa mazauna kauyuka, su bude asusun banki. “Akwai gidajen talakawa da ke bukatar abinci, ruwa, da sauran abubuwan more rayuwa.


Akwai bukatar nuna tausayi ga irin wadannan mutane. “Gidaje da dama a Najeriya su na bukatar tallafi domin yakar yunwa da kaucewa fadawa wahala,” a cewar Tinubu.

Kafin maganar tasa mutane da yawa suna ganin a baiwa mutane kuɗin ta asusunsu yafi komi zaman lafiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *