Spread the love

…an rufe karamar hukumar Dutsinma ba shiga ba fita

…an rufe manyan kasuwanni jihar Katsina

Daga Jamilu Dabawa, Katsina

Gwamnan jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari ya bada umurnin rufe garin Dutsinma, ba shiga ba fita daga karfe bakwai na safiyar Juma’a har sai illa Masha Allahu, sakamakon samun mutum daya dauke da wannan cutar da ta addabi duniya mai suna Malam Lawal Gwamna da ke unguwar kadangarun Dutsinma.

Haka kuma Gwamna Masari ya bada umurnin dakatar da sallah Juma’a daga sati mai zuwa. Haka kuma an dakatar da sallah tarawihi wadda ake lokacin azumi da Kuma dakatar da gudanar da Tafsirin azumi, da Kuma rufe kasuwanni masu ci mako-mako garin Mashi da Maiadua da Yar Gamji da Charanci da Jibiya da Dutsinma da Kagadama da Batsari da Sheme da Dandume da Kaita da Danja da Zango da Sabuwa da Mashi da Danja da Kuma Dankama, sakamakon bullar wannan cutar a jihar katsina.

Bayanin haka na kunshe cikin wata takardar manema labarai da Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, Alhaji Mustapha Muhammadu Inuwa ya sanyawa hannu, bayan kammala wani taron masu ruwa da tsaki a harkar tsaro a gidan Gwamnatin jihar Katsina.

Masari ya kara da cewa an dakatar da Sallar Tarawi, wadda ake yi cikin azumin watan Ramadan da Kuma Tafsirin a Massallatan jihar Katsina da kuma saura wurare zaman al’ummar.

Sanarwa ta cigaba da cewa an dakatar da gidajen cinema da kuma gidajen kallace-kallace kwallo da Fina finai. Haka kuma masu an rufe shigowa jihar Katsina daga makwabtan jihohi wanda aka ba jami’an tsaro su tabbatar da hakan.

Gwamna Masari ya ce Wannan matakai da gwamnatin ta dauka, ta yi shi ne domin ganin jihar Katsina ta dakile yaduwar cutar da Kuma kiyaye lafiyar al’umma jihar.

Daga karshe Gwamna Aminu Bello Masari ya yi kira ga al’ummar jihar Katsina su zamanto masu biyayya ga wannan dokar. Su zamanto masu bin shawarwarin masana kiwon lafiya. Da kuma cigaba da Addu’o’i domin kawo karshen wannan annobar ta Covid 19.

Yanzu da jihar Katsina, ta samu mutum bakwai da aka tabbatar da su na dauke da cutar, daya ya rasu, sauran kuma an killace su.

Wannan cutar ta fara gwadawa yankin Arewa boni ta fara ci kamar wutar daji.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *