Majalisar Zartarwa ta Jihar Sokoto wadda Maigirma Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ke jagoranta ta rage Kudin Kasafin Kudin 2020 da kashi 25% saboda giɓin da aka samu a duniya baki ɗaya kan cutar Korona, daga Naira Biliyan 202 zuwa Naira Biliyan 153.


Haka ma Gwamnatin jihar Sokoto ta umurci Ma’aikatar Filaye da Gidaje da su fara tantance masu sana’a da kasuwanci bisa ƙa’ida dake kan titin tashar Illela zuwa More wanda za’a ba da kwangilar yin titi mai hannu biyu don biyan su diyya da kuma samar masu sabon mazauni.

 
Kwamishinan yaɗa labarai Isa Bajini Galadanchi ya ce Majalisar Zartarwa ta aminta da soke biyan kudin ruwan sha ga maaikatan gwamnati da sauran jamaa jiha har na tsawon wata 2   Afrilu da Mayu. Don sauƙaƙa halin da cutar  ta haifar.

 Kwamishina ya ce  Majalisar  ta aminta da Soke kwangilar gina Gidan Mataimakin Gwamna na gwamnati dake Kaduna Road wanda aka bayar shekarun baya kuma Dan kwagilar yayi watsi da aikin. Don haka an bada dama a nemo wani don yayi kammala aikin.

Ya ce an  aminta da rahoton da Kwamitin da aka kafa don gano yadda Makarantun Gaba ga Sakandare a Sokoto Wato Tertiary Institution ke karbar kudaden Haraji da kuma yin amfani da shi, inda daga 1 ga watan Mayu 2020 asusun hada kudin zai zamo guda kuma Makarantun idan sun taro haraji za su dauki kashi 60% inda Gwamnatin jiha zata dauki kashi 40%. 

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *