Kansila ya sace Kayan abincin da aka bashi domin ya rabawa jama’ar yankinsa a Neja

Kansila ya sace  Kayan abincin da aka bashi domin ya rabawa jama’ar yankinsa a  Neja

Wani Kansila a karamar hukumar Katcha ta jihar Neja ya bace ɓat da kayan abinci da aka ba shi ya rabawa mutanen yankinsa domin saukake radadin dokar zama a gida da gwamnati ta sanya kamar yadda TheNation ta ruwaito.


Gwamnatin jihar ta sanya dokar ta baci ne domin takaita yaduwar cutar Coronavirus a jihar. 


An nemi Kansilan an rasa bayan bashi buhuhunan kayan hatsi 30 da aka bukaci ya rabawa mutane. 


The Nation ta tattaro cewa Kansilan na cikin kwamitin da aka nada domin rabawa mutane kayan masarufi a yankin. 


Sakataren gwamnatin jihar wanda shine shugaba kwamitin yakin COVID-19 a jihar, Alhaji Ahmed Ibrahim Matane, ya tabbatar da aukuwan haka kuma yace wannan abin takaici ne.


Alhaji Ahmed Ibrahim ya nuna bacin ransa kan abinda Kansilan yayi inda yace yanzu al’ummarsa zasu sha wahala saboda halin ha’inci da rashin godiyan Allah na shugabansu. 


A cewar, an baiwa kowani yankin mazabu 274 dake kananan hukumomi 25 na jihar buhun Shinkafa 10, Masara 10, da Gero 10 kuma an nada kwamitocin rabawa a kowace karamar hukuma. “An nada kwamitoci a dukkan yankuna 274 dake jihar.


Kwamitin ya hada da Kansila, Mhugaban jam“iyya, Maigari, da Malamin addini domin rabawa mutane kayan hatsin.“ SSG Ahmed yace
Ya ce jamian tsaro sun bazama neman Kansilan kuma zai fuskanci fushin hukumar idan aka kamashi.


Wannan rashin imani ne ya nuna wanda hakan bai dace a samu shugabanni cikin irin halin na dabbobi ba.

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *