Spread the love

Shawara Zuwaga Honarabul Faruku Malami Yabo (Former Commissioner Of Local Government, Former APC Governatorial Running Mate.)
Ranka Yadade (With Due Respect,) na daɗe Inason In Baka Shawara Kuma Ban Sanka ba, bani da Direct Contact da kai amma nasan Idan na yi anan zaka Gani Insha Allah.
Ranka Yadade Wallahi Sakkwatawa Suna da Ra’ayi Da Tafiyarka, Sun Gamsu Dakai Kuma Soyayyarka Cikin Jinin Jikinsu Take.
Dayawa Cikin Mutanen Gari Kafin A Fadi Matsalarka Sau Daya Sai An Fadi Alkhairinka Sau Dari.


Har Wani Suna Nijji Anayimaka Wai Aljihun Ragga Ko Alu Na Biyu.


Shine Nike Ganin Wasu Abubuwa Da Ni Ina Ganin In Ba’ayi Gyara Garesu Ba Zasu Iya Kawomaka Cikas Gameda Ambition Da Kakeda Shi Na Siyasa.


A Matsayina Na Dan APC Kuma Mai Ra’ayi Da Irin Salon Tafiyar Siyasar Gidanka, Nikeson Inyi Amfani Da Wannan Damar In Sanar Dakai Matsalar Da Wata Kila Kai Baka Hankalta Da Ita Ba.


Maganar Gaskiya, Kuma Ita Gaskiya Babu Mai Gayamaka Ita Sai Masoyinka, Ba Lallai Bane Lokachin Da Aka Fadi Gaskiyar Tayima Wanda Ake Gayama Ita Dadi Ba.


Na Lura Da Cewa Tun Sadda Allah Ya Jarabcemu Da Faduwa Za6e Ban Sake Ganin Kayi Sati Biyu Masu Kyau Ba A Garin Sakkwato, Wanda Wannan Sam Bai Dace Da Dan Siyasa Mai Ambition Ba.


Dan Siyasa Na Kwarai Shine Wanda Yake Tareda Talakkawanshi Komai Wuya Komai Dadi, Ko Lokachin Siyasa Ko Babu Siyasa.
Ba Lallai Bane Sai Ka Ba Mutum Kuddi Ba, Shi Masoyinka Mai Sonka Tsakani Da Allah Ba Kuddinka Yakeso Ba.


Shidai Babban Abinda Yake Bukata A Wurinka Yazama Yana Ganinka Kana Yin Intervention A Cikin Lalurorinshi.
Misali Gaisuwar Rasuwa, Zanen Suna, Daurin Aure Da Sauran Su.


A Cikin Haraka Ta Siyasa Ba Samun Mutane Bane Keda Wuya, Babban Abinda Yakeda Wuya Ga Harakar Siyasa Shine Ya Za’ayi Kayi Maintaining Mutanenka Yazama Basu Watse Suka Barka Ba.


Zan Iya Yimaka Uzuri Saboda Bansan Irin Commitment Da Suke Gabanka Na Business Da Sauran Rayuwarka Ba.


Amma Wannan Bazai Hana Ace Karkashinka An Qirqiri Wani Foundation Ba Wanda Zaici Gaba Da Kulawa Da Lamurranka Ko Baka Nan Ba.


Sanin Kowane A Garin Sakkwato Kana Cikin Manyan Yan Siyasar Da Allah Ya Azzirta Da Yan Social Media Wayanda In Sunyi Rubutu Ko Ina Yana Kaiwa.


Yakamata Abasu Dama Sucigaba Da Tallata Manufofinka Ko Baka Nan.
Shidai Mulki Allah Yake Bayar Dashi Ga Wanda Yaso Sadda Yaso Batareda Yayi Shawara Da Kowaba:
قُلِ اللَّهُمَّ مَالِكَ الْمُلْكِ تُؤْتِي الْمُلْكَ مَن تَشَاءُ وَتَنزِعُ الْمُلْكَ مِمَّن تَشَاءُ وَتُعِزُّ مَن تَشَاءُ وَتُذِلُّ مَن تَشَاءُ بِيَدِكَ الْخَيْرُ إِنَّكَ عَلَىٰ كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ


Sannan Ita Daukaka Allah Yake Daukaka Wanda Yaso:
نَرْفَعُ دَرَجَاتٍ مَّن نَّشَاءُ.

Sannan Da kai Da Ahmed Aliyu Da Duk Wani Maison Wannan Kujera Ta Gwamnan Sakkwato Allah Ya riga Yasan Wanda Zai Samu.
Amma Shari’a Bata Hana Mutum Yayi Lalabe Ba.


Haka Kuma Doka Tabada Dama Ga Dan Kasa Yafito Ya Nemi Kujerar Da Yake So Matukar Yayi Qualifying.


Allah Yasa Wannan Saqon Ya Isa, Kuma Allah Yabada Ikon Dubawa Da Kuma Daukar Matakin Gyara.

Rubutawa:
Dan Almajiri.

Wannan ra’ayin shi ne Managarciya ta ɗauko a turakarsa domin sanar da Sakkwatawa akwai wani motsi da masoyan wannan ɗan siyasar ke son ya yi, duk da shi ya ɓoye kansa kan wani dalili da bai bayyana musu ba, wanda suke buƙatar sani kafin su yi masa uzuri.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *