Spread the love

Managarciya ta samu labari da ba ta tabbatar ba, cewa akalla mutane 17 ne suka mutu yayin da jirgin yakin Nijeriya ya jefa bama-bamai a kauyen Sakotoku dake karamar hukumar Damboa ta jahar Borno, bisa kuskure, kamar yadda TheCable ta ruwaito.

Jaridar TheCable ta ruwaito wadanda suka mutu a wannan harin su ne mata da kuma kananan yara, wanda suke wasa da zaman shan iska a karkashin wata bishiyar mangwaro a garin.

Majiyoyi daga gidan Soja sun bayyana an jefa bamabaman ne bayan rundunar Sojan sama ta samu labarin taruwar ‘yan Boko Haram a kauyen, don haka ta shirya musu luguden wuta. 

Inda ya kamata a kai harin shi ne wani yanki a Korongilum dake makwabtaka da Sakotoku da kimanin nisan kilomita 12, a nan ne mayakan Boko Haram din suka taru.

Rundanar sojan Nijeriya a yanzu ta kara tashi tsaye wajen ganin ta kai karshen mayakan nan masu tayar da kayar bai a yankin Areawa ta Gabas.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *