Spread the love


Mai Girma Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR ya saka dokar hana zirga zirga a fadin jihar Kano wanda dokar zata fara aiki ne daga ranar Alhamis mai zuwa 16 ga watan April kuma dokar ta kwana bakwai ce a matakin farko. 

Gwamnati ta sa jami’an tsaro su tabbatar an bi wannan dokar a fadin jihar.An sanya dokar hana fita na mako guda a Kano.

Gwamna Ganduje ya ce dokar za ta fara aiki ne a daren ranar Alhamis da misalin karfe 10 na dare.


Haka ma Maaikatar Lafiya ta Jihar Kano ta bayar da sanarwar  samun karin mutum daya wanda ke dauke da cutar Korona.

Kwamishinan Lafiya na Jihar Kano Dokta Aminu Ibrahim Tsanyawa  ne ya tabbatar da haka.

Samun mutum dayan da aka yi a yau Talata ya sa Kano nada jimlar  mutane hudu masu dauke da cutar a jihar.

Wannan matakin na buƙatar gwamnati ta fito da hanyoyin tallafawa talakawa da kayan abinci da masarufi domin mafiyawan mutane sai sun fito ne suke samun abin da za su sanya a bakinsu.Akwai buƙatar gwamnati ta duba halin yunwa da mutane ke ciki ita ma babbar matsala ce mai kisa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *