Spread the love

Shugaban rundunar sojojin Nijeriya Janaral Yusuf Tukur Buratai ya nuna kudirin da yake da shi na ba zai bar shingen mayakan rundunar Lafiya Dole har sai an kammala da ‘yan ta’addar kungiyar Boko Haram kwata-kwata a yankin Arewa ta Gabas.

Jaridar Nation ta ruwaito cewa da farko Buratai ya ba da sanarwar ya koma yankin Arewa ta Gabas bayan sojojin Chadi sun fatattaki mayakan na Boko Haram daga kan iyakarsu.

Shugaban wanda ya yi bukin Easther tare da sojojinsa ya nuna damuwarsa yanda tayar da kayar bai ta dauki dogon lokaci a Nijeriya, amma ya ba da tabbacin za su kare da mayakan Boko Haram.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *