Spread the love

Aishatu Bashir Tambuwal
aishabasheer2017@gmail.com


Assalamu alaikum uwargida da amarya da matan da ke gidan iyayensu, barka da wannan lokacin, da fatar na same ku lafiya.


Ayau dai a cikin zauren GIRKE_GIRKE na zo muku da Yadda ake yin SARKIN DAƊI nasan uwar gida za ta so ta ji yanda ake wannan haɗin, to ki biyoni a madafata.
KAYAN HAƊI
-nama
-ƙwai
-tafarnuwa
-gishiri da maggi
-curry
-mai

HAƊI:

Ki samu naman ki ɗanye Mai kyau Wanda bashi da kitse ko Kashi tsoka zallah , sai ki daka ko kiyi blending sai ki saka attarugu Maggi curry tafarnuwa sai ki daka su tare , bayan ya daku ki kwashe ki zuba su a Leda ki kukkule kamar za ki yi alala , sai ki zuba ruwa a tukunya, ki sassaka a ciki ki dafa kamar dahuwar alala idan yayi kamar minti 15 zuwa 20 sai ki sauke ki barshi ya huce sannan sai ki ciccire Naman daga ledar za ki ga Yana fitowa kamar alala ya haɗe jikinsa , sai ki saka wuka ki yanka su ‘shape’ ɗinda kike so, sai ki fashe ƙwai dai dai Wanda zai ishe ki suya, sai ki rinƙa tsomawa kina soyawa da ruwan Mai.

Za a iya yi kowa mai gida da mahaifi Barka da Shan ruwa da wannan hadin, a ci daɗi lafiya.

Tsakure:

Mukan kawo bayani kan nau’in abinci daban-daban domin amfanin kanmu da kanmu musamman mata masu biyar shafin wannan mujallar.

Ba kawai mu sanar da su labaran da halin duniya ke ciki ba, sai mu haɗa masu da abin da zai taimaki zaman gidansu da gidan mijinsu don ƙara samun haɓakar wayewarsu.

Mun kiyaƴe sosai a wurin kawo abinci ba mu sanar da abincin da bai gina jiki domin muna son mu riƙa koyar da abin da kula da lafiyar makarantanmu, a kodayaushe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *