Spread the love

Kungiyar dalibai musulmai ta Nijeriya ta yi kira ga Tambuwal ya samar da hanyoyin rage radadin zama gida ga mutanen Sokoto

Daga Mukhtar Haliru Tambuwal Sokoto. 

Kungiyar dalibbai musulmai ta kasa  reshen jihar Sokoto karkashin jagorancin  Alhaji  Abubakar Sadik Isa  ta sanar da jingine duk wani taro ko aikin kungiyar har sai wani lokaci.

Kungiyar ta sanar da hakan ne a zaman da mambobin Zartarwar kungiyar suka yi  da yammancin ranar Alhamis 9 April,2020, a Ofishinsu dake birnin sokoto.

shugaban ya bayyana cewa “mun dakatar da duk wasu Shiraruwa da tarukkan  mu bisa ga umurnin da gwamnatin sokoto ta ba da na adakatar da duk wasu tarukka zuwa wasu sati biyu masu zuwa.”

Kungiyar ta yabawa gwamnatin jihar sokoto da Majalisar Mai martaba sarkin musulmi akan kokarin da akeyi na dakile yaduwar cutar corona, musamman na ba da damar  cigaba da sallah, Kasuwanni da sauran su.

Shugaban ya shawarci Alummar Musulmi da su bi shawarwarin da masana ke bayarwa dan kaucewa kamuwa da cutar, Kana yayi Kira ga Al-Ummar Musulmi da a himmantu da Addu’a kana a guje sabawa Allah, a Kuma tuba da sabo dan Allah ya karbi Addu’ar.

A bangaren dalibbai an shawarce su da su himmantu da karatun domin samun nasarar jarabawar da za su rubuta da sun koma makaranta, Kuma su taimakawa iyayensu a zaman su nagida.

Haka Kuma kungiyar ta yi Kira ga gwamnatin jihar Sokoto da ta fito da wasu hanyoyin da za’a ragewa Alummah radadin wannan zaman gida, musamman ga Maras galihu. 

Wannan bayanin an same shi ne ta hannun jami’in hulda da jama’a na kungiyar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *