Spread the love


Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ƙara wa’adin hana fita a Abuja da Lagos da Ogun zuwa wasu sati biyu masu nan gaba.

Shugaba Buhari ya ba da sanarwar ne a jawabin da ya yi wa al’ummar ƙasa kan hali da matakan da gwamnati ke ɗauka kan annobar cutar Korona.

A sati biyu da suka wuce sun ɗauki matakai na rage raɗaɗin halin da ake ciki sun raba abinci da kuɗi a ƙasa da bayar da bashin da mutane za su sake biya daga baya amma an yafe masu don sauƙaƙa raɗaɗin da ake ji cikin wannan mawuyacin hali.

Buhari ya ce za a cigaba da ɗaukar matakan ba za a tsaya ba bayan mutane miliyan 2.6 na farko da hwamnati za ta tallafawa ya ba da marnin sake sanya wasu mahidanta miliyan ɗaya yawan mutanen zai kai 3.6 miliyan kuma mutanen za su amfana cikin sati biyu nan masu zuwa.

Ya kira wasu ministocinsa da zauna domin fito da hanyoyin da za su sanya a samu damar yin noma a wannan daminar mai kamawa, ana son samun sauƙin noma a wannan yanayin annobar Korona.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *