Spread the love

A daren yau litinin Gwamnatin jihar Kano ta kara tabbatar da samun mutum biyu dauke da COVID-19 a jihar.

Ma’aikatar lafiya ta jihar Kano ce ta wallafa hakan a shafinta na twitter a daren yau litinin.

Manema labarai sun ruwaito cewar samun mutune  biyun na yau ya tabbatar da cewar mutane uku ne ke dauke da cutar ta COVID-19 a jihar Kano.

Haka kuma Wasu Kungiyoyi Kare hakkin Dan Adam karkashin jagoranci comrade  A A Haruna  Ayagi dakuma takwaransa wato Karibu Yahaya Lawal Kabara su ne suka yi hira da manema labarai  in da suka ce mutumin mai suna Kabiru Rabi’u Dan Sitta Ya yi gangancin shigowa Kano duba da halinda ake ciki. 

Ya zama wajibi sukai shi zuwa kotu da zarar ya sami sauki duba da yadda ya jefa mutanan Kano cikin fargaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *