Spread the love

Yansanda jihar zamfara sun tabbatar da cewa jinin da aka samu a gidan tsafi a Gusau na bil’adam ne.

Daga Aminu Abdullahi Gusau

Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara sun tabbatar da cewa, jinin da aka samu a gidan tsafi a Gusau, sun tabbata jinin ɗan ‘Adam ne, bayan da akai samfurin jinin aka auna.

Wannan bayanin ya fito daga bakin kakakin rundunar, sufurtanda ‘yan sanda, Shehu Mohammed, lokacin da yake zantawa da manema labarai a garin Gusau.

SP, Shehu yace, kamar yadda suka bada tabbacin cewa za su yi wa jama’a bayani bisa ga cigaba da aka samu na binciken kwakwaf da suke yi bisa ga wannan aikin na matsafa, ya ce sun dauki wannan kwarya Mai dauke da jinin inda suka kai wajen Ma’aikatan sanin lafiyar jini kuma suka tabbatar masu cewa jinin mutun ne.

“Mun dauki samful din jinin muka kai a wajen da ake auna nau’in jini, kuma suka tabbatar muna cewa wannan jinin na mutun ne, kuma kalar sa tana cikin group (0) Mai karfi.”in jishi.

Kakakin ya kara da cewa, har yanzu ana nan ana ci gaba da bincike, “Yanzu haka mun kama mutane wayanda keda alaka da wannan aika aikar, idan muka kai karshen binciken mu zamu sanar da kowa abinda ke ciki.”ata bakinsa.

Idan baku manta ba, ranar Talata data gabata ne, Kwamishinan yansanda na wannan jihar Alhaji Usman Nagogo, yayi taron Yan jarida a hedikwatar yansanda dake nan Gusau domin sanar da al’umma kamawa da rushewar wani gida da ake tuhumar matsafa ke ciki.

A cikin gidan, an samu kayan tsafi daban daban, harda wannan kwarya wadda cike da jini, da kuma takardu wayanda ke dauke da sunayen wasu jiga jigan wannan gwamnati, kuma ansamu wata tukunya wadda aka sokawa allurai a jikin ta,da dai sauran su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *