Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya tabbatar da tsoho mai shekara 75 wanda yake tsohon jekada ne ya kamu da cutar ta Korona wadda aka yi wa laƙabin COVID19.

Ganduje ya ce gwamnati  ta tura domin duba yanayin jinin mutum 10 da ake zargi da cutar  a Abuja kwana uku da suka wuce 9 daga cikinsu ba su dauki da cutar, amma an samu ɗayan waton tsohon jekada yana dauke da ita.

Ganduje ya yi magana a gidan  Afrika cikin gidan gwamnati ya bayyana wannan lamarin amatsayin abin baƙin ciki, don haka gwamnati za ta dauki matakin da za ta tabbatar lamarin bai gagari kundila ba.

Ya bayar da umarnin adaidaita sahu ta riƙa daukan mutum ɗaya koeace a matakin da za a dauka na hana yaɗuwar cutar.

A cewarsa a wannan hali ina bakin cikin sanar da mutanen Kano Yau Assabar mun samu mun samu maras lafiya da ke dauke da cutar Korona.

Ɗan shekara 75 tsohon jekadan Nijeriya ne, ys yi tafiya zuwa Kaduna da Lagos da Abuja, sannan ya dawo Kano a 25 ga watan Maris na 2020.

Ya ce maras lafiya a Kurma Dawakin Kudu cibiyar da ake killace masu cutar domin basu kulawa.

Yanzu gwsmnati na kokarin ta gano wadan da ya yi hulda da su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *