Spread the love

Kungiyar Kwadago ta gargadi gwamnatin tarayya kar su kori ma’aikata a kasar Nijeriya saboda cutar Korona ta kawo wa tattalin arziki cikas.

Shugaban kungiyar na kasa Kwamared Ayubba Wabba a sakon fatar alheri kan bukin Esther, kare hakkin ma’aikata da samar da wasu abun da yakamata a maida hankali na wannan lokacin na Korona.

Wabbba ya fahimci samar da aiki ma ne zai kara taimakon kasa ga cigaban rayuwarta.

Masana a bangarori da dama sun bayyana tattalin arzikin masana’antu masu zaman kansu ya tabu sosai, da yawansu na ta kokarin yanda za su cigaba da rayuwa.

Bangaren aikin yi na Amerika ma sun fitar bayanin sun rage ma’aikata sama da dubu 700 a watan Maris da ya gabata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *