Spread the love

An yi sulhu tsakanin hukumar tace fina-finan Kano da Arewa24


Hukumar tace fina-finai ta jihar Kano da gidan talbijin na Arewa24 sun yi sulhu game da takaddamar da ta taso kan nuna fim din ‘Kwana Casa’in’.


Shugaban hukumar, Isam’ila Na’abba Afakalla ne ya bayyana haka a sakon da ya fitar ranar Juma’a.


A cewarsa, “Bayan zama da aka yi tsakanin hukumar tace fina-finan Kano da jami’an gidan talbijin na Arewa24 jiya Alhamis da yau Juma’a, an kai ga matsaya inda aka amince za a cire bangarorin da suke dauke da abubuwan da al’umma ke korafi a kai.”
Ya kara da cewa gidan talbijin na Arewa24 ya amince cewa nan gaba ba zai sake nuna wani fim din Hausa ba sai “ya kasance wanda yake da shaidar tantancewa da ta fito daga hukumar tace fina-finai.”


A ranar Talata ne hukumar tace fina-finai ta jihar Kanon ta fitar da sanarwar dakatar da ci gaba da nuna shirin Kwana Casa’in da shirin Gidan Badamasi wadanda suka yi tasiri sosai ga dimbin masu kallo a sassan duniya.


Isma’ila Na’abba Afakallah ya shaida wa BBC cewa fina-finan biyu sun ci karo da tsarin dokokin hukumar, inda ya ce a shirin ‘Kwana Cas’in’ an nuna maza suna cacumar wata yarinya.


A shirin Gidan Badamasi kuma ya ce an yi amfani da kalaman da ba su dace ba, wadanda dukkaninsu a cewar Afakallah sun saba wa sashe na 102 na dokar da ta kafa hukumar tace fina-finai a 2001.


Duk da cewa kafar Arewa 24 ba ta ce komi ba, ko fitar da sanarwa game da matakin dakatar da shirye-shiryenta da aka yi, amma kafar ta wallafa bidiyon dandanon shirin da za a nuna mako na gaba a shafinta na Twitter, kwana guda bayan dakatar da nuna shirin da hukumar tace finafinai ta Kano ta yi.


Shirin Kwana Casa’in wasu kungiyoyin duniya da hadin gwiwar gidauniyar MacAurther ne ke daukar nauyinsa, yayin da kuma Falalu Dorayi ne furodusan shirin Gidan Badamasi.


Labarin dakatar da shirye-shiryen bai yi wa dumbin masu kallo dadi ba, inda ake ganin babu wani shiri da ake yawan kallo da ake nunawa a wata kafar talabijin a arewacin Najeriya kamar sa.


Shirin Kwana Cas’in ya shafi siyasa da kuma bankwado yadda rashawa ta yi katutu a harkokin gwamnati, wani dalilin da wasu ke ganin shi ya sa gwamnatin Kano ta yi amfani da hukumar tace fina-finai aka dakatar da nuna shirin.


Kazalika shirin na nuna irin yadda wasu talakawa suke da hadama da rashin gaskiya a mu’amalarsu ta yau da kullum.
Shirin ya kayatar matukar gaske abu ne da ake ta alfahari da shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *